in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane a kalla 12 a Najeriya
2015-07-16 09:45:21 cri

Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane a kalla 12 sakamakon wasu hare-hare da mayakan Boko Haram suka kaddamar ranar Talata a garin Warsala da ke kan hanyar Borno zuwa jihar Yobe.

Bayanai daga yankin na cewa, mayakan sun yi wa garin kawanya ne inda suka rika kona gidaje da ababan hawa, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Bugu da kari 'yan sandan yankin sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin aukuwar lamarin, amma ba su yi wani karin haske game da adadin mutanen da wadannan hare-hare suka shafa ba.

Ko da a ranar Larabar da ta gabata ma mayakan na Boko Haram sun kai hari garin Damasak a jihar Borno wanda ke kan iyaka da Najeriya da Nijar, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin arcewa zuwa yankunan jamhuriyar Nijar. Sai dai babu wanda ya jikkata sanadiyar harin.

Alkaluma na nuna cewa, kimanin mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da mayakan na Boko Haram suka kara zafafa hare-haren da suke kaiwa kan fararen hula a farkon watan Yuni, musamman ma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar ta Najeriya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China