Babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, ya alkawarta sake farfado da yakin da sojojin kasar ke yi da Boko Haram a yankunan arewa maso gabashin kasar.
Olonishakin wanda ya bayyana hakan a Abuja, fadar mulkin kasar, yayin bikin karbar ragamar aiki daga tsohon hafsan hafsoshin sojin kasar Alex Badeh, ya ce, nan gaba kadan zai gana da manyan hafsoshin sojin Najeriyar, da ma sauran dakarun kasar, domin bullo da sahihiyar hanyar sauya yanayin da ake ciki ta fuskar tsaro.
Manjo Janar Olonishakin, ya kara da cewa, sabon jagorancin rundunonin sojin kasar zai yi iyakacin kokari, na murkushe ayyukan ta'addanci a dukkanin sassan arewa maso gabashin Najeriya.
A wani ci gaban kuma, hafsan sojojin ruwan kasar mai barin gado Vice Admiral Usman Jibrin, ya ce, ya zuwa watan Yunin wannan shekara, rundunar ta cimma nasarar rage yawan satar danyan-man kasar daga ganga miliyan 2.4 a ko wane wata cikin shekarar bara, ya zuwa ganga 300,000. Jibrin ya bayyana hakan ne yayin da yake mika ragamar aiki ga sabon hafsan rundunar ruwan kasar Rear Admiral Ibok-Ette Ibas.
A fannin rundunar sojin sama kuwa, sabon hafsan ta Air Vice Marshal Sadeeq Abubakar, ya alkawarta dorawa daga inda Air Marshal Adesola Amosun mai barin gado ya tsaya, yana mai cewa, zai matsa kaimi wajen inganta daukar matakan soji a yankunan arewa maso gabashin Najeriya. (Saminu)