in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda a Najeriya sun gano wasu makamai daga mayakan Boko Haram
2015-07-23 09:23:31 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, ta ce, ta gano wasu tarin makamai da suka hada da bindigogi, da harsasai da kuma bama-bamai cikin wata motar mayakan Boko Haram.

A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar ta Yobe Markus Danladi, jami'an 'yan sandan na gudanar da binciken ababen hawa ne a ranar Litinin, a kan babbar hanyar da ta hada birnin Damaturu zuwa Maiduguri, lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake biyar suka lura cewa, za a gano su, sai suka tada bam dake cikin wata mota kirar Jeep da suke ciki, inda nan take suka hallaka kansu, da kuma wasu 'yan sanda 3, kana wasu 'yan sandan 2 suka samu raunuka.

Har wa yau kwamishinan 'yan sandan ya bayyana gano wasu karin makamai iri daban daban daga mayakan na Boko Haram, wadanda jami'an tsaro suka dakile shirinsu na kaddamar da hari kan garin Bara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China