in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Zulu ya musunta hura wutar korar baki
2015-04-19 17:14:28 cri
A jiya Asabar 18 ga wata, sarkin Zulu na kasar Afirka ta Kudu, Goodwill Zwelithini a cikin jawabinsa ya musunta hura wutar korar baki 'yan kasashen waje.

A wannan rana, yayin da yake halartar wani biki a yankin Jozini dake lardin KwaZulu-Natal, Goodwill Zwelithini ya bayyana cewa, bai yi magana irinta kin jinin baki 'yan kasashen waje ba, balle ma ya ta da husuma tsakanin jama'ar kasar da mutanen kasashen waje. Yace an yi kuskure wajen fahimtar maganar da ya yi a da, a hakika dai, ma'anarsa ita ce sa kaimi ga jama'ar kasar da su yi gwagwarmaya da talauci, su kokarta a fannin aikin noma.

Ban da haka, Goodwill Zwelithini ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su halarci taron da ya shirya domin kawo karshen rikici iri na nuna kiytayya ga baki 'yan kasashen waje. Za a kira taron a gobe litinin 20 ga wata a birnin Durban, inda sarkin Zulu da kuma sarakunan sauran kabilu za su halarta.

Bisa labarin da kafofin yada labarai na wurin suka bayar, an ce, a ranar 20 ga watan Maris, Goodwill Zwelithini ya yi jawabinsa a fili, inda ya bukaci 'yan waje da su koma kasashen su nan take, sabo da a ganinsa, zuwansu ya kwace guraben aikin mazauna wurin, yayin da mutanen sauran kasashen Afirka suka zo yin ciniki a nan, hakan ya tsananta yanayin da ake ciki na rashin samun aikin yi a kasar Afirka ta Kudu, ta yadda jama'ar kasar suke kara fama da kangin talauci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China