Wasu kasashen Afirka sun bukaci Afirka ta Kudu da ta kawo karshen tashin hankalin kasar
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar Afirka ta Kudu, dangane da lamarin, wasu kasashen Afirka sun bukaci gwamnatin kasar Afirka ta Kudu da ta dauki matakai yadda ya kamata domin kawo karshen tashe-tashen hankula da nuna kyamar baki a kasar, haka kuma, kiyaye tsaron mutanen ketare dake kasar.
Bugu da kari, kasashen Kenya, Somaliya, Malawi, Zimbabwe da Mozambique da wasu kasashen Afirka sun nuna damuwarsu matuka kan yanayin kasar Afirka ta Kudu, inda suka kuma bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakai domin yaki da laifuffuka da kuma kiyaye tsaron mutanen ketare.
Tuni ma dai wasu kasashen Afirka sun riga sun fara kwashe mutanensu daga kasar, yayin da wasu suke shirya yin hakan. (Maryam)