in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun hallaka kimanin 43 a Najeriya
2015-07-15 09:57:46 cri

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya mai fada da rikicin Boko Haram na cewa, a kalla mutane 43 ne suka mutu bayan da wasu 'yan bindiga suka aukawa wasu kauyuka guda 4 a karamar hukumar Monguno.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno Aderemi Opadokun ya tabbatar da aukuwar haren-haren da suka faru a karshen mako, sai dai bai yi wani karin haske game da yawan mutanen da wadannan hare-haren suka rutsa da su ba.

Amma wasu jami'ai a yankin sun bayyana cewa, adadin na iya karuwa sakamakon munanan raunukan da suka ji sanadiyar hare-haren da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kaddamar.

Wani basarake a yankin mai suna Baba Maigoro ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kayayyaki.

Alkaluma na nuna cewa, kungiyar ta hallaka mutane sama da 13,000 tun lokacin da ta fara wannan aika-aika a shekarar 2009, inda ta ke kaddamar da hare-harenta kan fararen hula, tare da matsa lamba ga gwamnati. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China