in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ian Khama ya sake lashe zaben shugaban kasar Botswana
2014-10-26 17:12:36 cri

Babban alkalin kotun kolin kasar Botswana, Maruping Dibotelo ya sanar a safiyar ran 26 ga wata cewa, jam'iyyar BDP dake rike da shugabancin kasar ta sami fiye da rabin kujeru a majalisar dokokin kasar, hakan ya nuna cewa dan takararta shugaba mai ci na yanzu Ian Khama ya sake tazarcewa.

An gudanar da babban zabe karo na 11 tun bayan da wannan kasa dake kudancin Afrika ta samun 'yancin kai. Bisa ka'idar wannan zabe, masu kada kuri'u sun zabi 'yan majalisun dokoki 57 kai tsaye, dan takarar da ya fito daga jam'iyyar da ta samu fiye da rabin kujerun zai zama shugaban kasar. Yayin da aka bayyana wannan sakamako, jam'iyyar BDP ta samu kujeru 29, lamarin da ya bata damar lashe zaben.

Botswana ta samu 'yancin kai a shekarar 1966, jam'iyyar BDP ta lashe dukkan zabubbuka da aka yi a wannan kasa. Za a gudanar da bikin rantsar da Khama a ran 28 ga wannan wata da muke ciki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China