in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara babban zabe a kasar Botswana
2014-10-24 20:18:00 cri
A yau ne aka fara zaben shugaban kasa da sabbin 'yan majalisun dokoki a kasar Botswana.

An bude tashoshin kada kuri'a tun da misalin karfe 6 da rabi na safe zuwa karfe 7 na yamma agogon wurin, inda ake saran mutane 824,073 da aka yi wa rijistar kada kuri'a za su zabi 'yan majalisun dokoki 57 da kansilolin kananan hukumomi 490.

Dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar BDP da ke rike da ragamar shugabancin kasar tun lokacin da ta samu 'yanci a shekarar 1966, kana shugaban kasar mai ci Seretse Khama Ian Khama ne ake saran zai lashe zaben. Koda yake jam'iyyar tana fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar adawa ta UDC da ke kawance da sauran jam'iyyu.

Kungiyoyin SADC, AU da EU sun isa kasar don sa –ido kan zaben da za a gudanar.

Kasar Botswana dai tana daga cikin kasashen Afirka da ke da zaman lafiya na siyasa, kana kasar da ke kan gaba a duniya wajen samar da ma'adinin lu'u-lu'u. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China