A jawabinsa bayan rantsar da shi Ian Khama ya ce da shi da sauran sabbin 'yan majalisar dokokin kasar da aka zaba da na kananann hukumomi suna da nauyi a wuyansu na samar da jagoranci mai kyau inda zasu saka bukatun kasar a gaban kome.
Al'ummar kasar Botswana dai sun kada kuri'unsu ne a ranar jumma'ar da ta gabata domin zaben 'yan majalisun dokoki 57 da kuma kansilolin kananan hukumomi 490, inda aka sake zaben Ian Khama a matsayin shugaban kasar bayan da jami'iyyar sa dake mulki BDP ta lashe zaben da samun mafi rinjaye a kujerun majalissar dokokin.(Fatimah Jibril)