Tawagar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, sabuwar dokar da aka kafa za ta ba da damar gudanar da harkokin tsaron kasar Sin bisa doka. Tana ganin cewa, da farko dai, an tsara dokar ce da nufin tinkarar kalubalolin da ake fuskanta a fannin tsaro, gami da kokarin gudanar da harkokin mulki bisa doka.
Sa'an nan na biyu, tsara dokar tsaron kasa wata al'ada ce da kasashe daban daban suke bi, yayin da dokar tsaron kasar Sin ta dace da muhallin kasar, da ka'idojin kasa da kasa, haka kuma an yi koyi da nagartattun fasahohi na kasashe daban daban a kokarin tsara ta.
Abu na uku da tawagar kasar Sin ta bayyana cikin sanarwar shi ne, duk wata kasa ko kuma al'umma, tilas ne ta yi kokarin samun daidaituwa tsakanin hakkin mutane da nauyin dake bisa wuyansu. Sabili da haka, sabuwar dokar da kasar Sin ta tsara ta kayyade wasu abubuwa dangane da iko da nauyin dake bisa hukuma, gami da daidaikun mutane da kungiyoyi. Haka kuma na hudu, a cewar tawagar kasar Sin, an tsara wannan doka ce don tabbatar da kare hakkin dan Adam, ganin yadda dokar ta jaddada manufar tabbatar da tsaron jama'a, ta kuma kayyade cewa, duk wani matakin da za a dauka a fannin tsaron kasa, za a yi shi ne domin kare jama'a, sa'an nan za a dogaro kan jama'a don tabbatar da tsaron kasar.
A ranar 1 ga watan Yulin da muke ciki ne aka kaddamar da dokar tsaron kasar ta Sin.(Bello Wang)