in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Gabon da Chadi na tattauna batun yaki da kungiyar Boko Haram
2015-07-05 13:38:57 cri
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya kai ziyarar aiki a ranar Asabar a kasar Chadi inda ya samu tattaunawa ta sa'o'i uku tare da takwaransa na kasar Chadi Idriss Deby Itno kan batun yaki da kungiyar Boko Haram ta Najeriya.

Mista Ali Bongo ya isa wannan kasa, kwanaki 20 bayan tagwayen harin kunar bakin wake a birnin N'Djamena da suka halaka mutane 38, da suka hada da 'yan kunar bakin waken uku, tare da jikkata mutane kusan dari. A ranar 29 ga watan Yuni, kuma wasu mutane goma sha daya ne suka mutu wadanda suka hada da 'yan sanda biyar da 'yan kunar bakin wake shida, a yayin da wadannan 'yan kunar bakin wake suka ta da bama baman su a lokacin da 'yan sanda ke binciken wani gida.

"Na zo domin in nuna goyon bayana da na kasar Gabon game da munanan hare haren baya bayan nan da suka faru anan birnin N'Djamena," in ji shugaban kasar Gabon bayan tattaunawa tare da shugaba Idriss Deby.

Haka kuma ya bayyana cewa sun maida hankali tare da takwaransa na Chadi kan yiyuwar tallafawa kokarin da Chadi da Kamaru suke yi wajen yaki da kungiyar Boko Haram. (Mamane Ada)

Baya ga batun soja, mun tattauna kan bangaren siyasa domin ta wace hanya za mu aiki domin fadada shirin mu, domin kawar da wannan annobar ta'addanci a cikin kasashen gamayyar tattalin arzikin kasashen Tsakiyar Afrika (CEEAC), in ji Ali Bongo shugaban kungiyar ta CEEAC a wannan karon. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China