Wata majiyar jami'an tsaron birnin ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua aukuwar wannan lamari, inda majiyar ta ce maharan sun yiwa gidan kurkukun birnin na Diffa dirar mikiya ne da sanyin safiyar jiya Lahadi dauke da muggan makamai, inda kuma nan take suka fara dauki ba dadi da jami'an tsaron dake gadi a lokacin.
An ce ga alama dakarun sun yi yunkurin fasa gidan yarin ne, sai dai hakar su bata cimma ruwa ba, domin kuwa sun shafe sa'o'i da dama suna fafata da jami'an tsaro kafin daga bisani a ci karfin su.
Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda kacal, bayan da wani maharin da ake zaton dan Boko Haram ne, ya tayar da wani Bam a wata kasuwa dake birnin N'Djamena fadar mulkin kasar Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16, ciki hadda jami'an tsaro, da kuma wanda ya kaddamar da harin. (Saminu)