in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gasar wasanni ta daliban jami'oi ta duniya karo na 28 a kasar Koriya ta Kudu
2015-07-09 10:04:09 cri

A daren ranar Juma'a 3 ga watan nan ne aka kaddamar da gasar wasanni ta lokacin zafi, ta daliban jami'oin duniya karo na 28 a Gwangju dake kasar Koriya ta Kudu, inda dalibai dubu 13, daga kasashe da yankuna 149 suka halarci gasar.

A cikin kwanakin 13 da za a shafe ana gudanar da gasar, za a lashe lambobin yabo na zinari 272 a wasanni 21. Kafin bude gasar, gwamnatin kasar Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, za ta yi kokarin tabbatar da gudanar da gasar yadda ya kamata, duk da bullar cutar MERS a kasar.

A ranar 3 ga wata da karfe 7 na dare ne aka kaddamar da gasar wasanni ta lokacin zafi, ta daliban jami'oin duniya karo na 28 a Gwangju dake kasar Koriya ta Kudu. A yayin bikin bude gasar, an gudanar da bikin maraba da zuwan 'yan wasa dalibai, da bikin shigowar tawagogin dabilai masu halartar gasar, da wasan nuna fasahohi, da kuma bikin kunna wuta. Bisa ka'idojin kungiyar hadin gwiwa ta wasannin daliban jami'oi ta duniya, shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye, ta sanar da budewar gasar a wannan karo.

"Ina sanar da bude wannan gasa ta wasannin lokacin zafi, ta daliban jami'oi ta duniya karo na 28 a nan Gwangju."

Kungiyar hadin gwiwa ta daliban jami'oi ta duniya ta ita ce ta dauki bakuncin gudanar da gasar wasannin, kana an kayyade daliban da shekarunsu ke tsakanin 17 zuwa 28, kuma basu wuce shekaru 2 da fara karatu a jami'oin ba wajen samun izinin shiga gasar.

An dai fara gudanar da gasar ne a shekarar 1959, kuma a wancan lokaci a kiran gasar da "gasar wasanni ta daliban jami'oi ta kasa da kasa".

Taken gasar a wannan karo shi ne "kyakkyawar makoma da aka kirkira".

A gun bikin bude gasar ta wannan karo, shugaban kungiyar hadin gwiwa ta daliban jami'oin duniya Claude-Louis Gallien, ya bayyana cewa an sanya burin matasa a gaban duniya, duba da cewa matashin yanzu ne zai zama shugaba a nan gaba. Gallien ya kara da bayyana ra'ayinsa game da duniyar wasanni wadda ke fuskantar rashin zaman lafiya a halin yanzu. Ya ce,

"Yanzu haka ana samun tashe-tashen hankula a duniyar wasanni, ya dace mu yi kokari a yayin gasar wasanni ta daliban jami'oi ta duniya, domin cimma burin canja wannan duniya. Kada kuma ku manta da koyi da 'yan siyasa, da masana kimiyya, da 'yan kasuwa, wajen canja duniya da kan ku."

Tun daga karshen watan Mayu, aka sau bullar cutar MERS a kasar Koriya ta Kudu. Ko da yake an samu sauki game da yaduwar cutar, amma duk da haka ya zuwa ranar 3 ga watan nan, an kara samun sabbin mutane da aka tabbatar da kamuwar su da cutar. Wannan lamari ya yi mugun tasiri ga gasar wasannin daliban jami'oin ta duniya a Gwangju. Amma duk da haka ya zuwa yanzu, ba a samu mutum ko daya da aka tabbata ya kamu da cutar a Gwangjun ba.

Don magance bullar wannan cuta, an kafa wata hukumar musamman ta bincike kan cutar, wadda hukumomi biyu masu killace masu dauke da cutar a birnin Gwangju suke gudanarwa, inda suke cikin shiri na karbar mutanen da ake zaton sun harbu da cutar.

Ban da wannan kuma, jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Koriya ta Kudu Gwon Deok-cheol ya bayyana cewa, an riga an shirya ayyukan kandagarki, da yaki da cutar MERS a filayen wasannin birnin. Ya ce,

"Tun daga ranar 29 ga watan Yuni, an tanaji tsarin binciken zafin jikin mutane, a asibitin kauyen 'yan wasa masu halartar gasar, wanda ke filayen wasannin, kana an horas da ma'aikata da suke amfani da wannan tsari. Kuma ya zuwa ranar 26 ga watan Yuni, an riga an gudanar da bincike kan yanayin lafiyar masu aikin sa kai fiye da dari da 43."

'Yan kasar Koriya ta Kudu su 516 ne dai suke halartar gasar wasannin ta wannan karo, wadanda kuma ake sa ran za su halarci dukkan wasannin da aka shirya a gasar, kana kasar na da burin samun lambobin yabo na zinari fiye da 25, inda matsayinta na samun lambobin yabo a gasar ya kai mataki na uku a jerin daukacin dukkan kasashe, da yankuna mahalarta gasar.

A nata bangare, kasar Sin ta tura tawagar mutane 596 domin halartar gasar, tawagar da ta kunshi 'yan wasa 380. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China