Bisa jimilla, Barca zai shafe shekaru 3 yana gudanar da wannan horo. Kuma zai rika daukar zababbun 'yan wasa matasa 15 zuwa 20, wadanda za su dace da matsayin kwarewa na kulaf din ya kai su Sifaniya, shirin da za a fara daga watan Afirilun shekara mai zuwa, kamar yadda jami'i mai kula da filin horoswar na Barca dake nan kasar Sin Zhao Wei ya bayyana.
Zhao Wei ya kara da cewa, da zarar zababbun 'yan wasan Sinawa sun isa Barcelona, za su fara taka leda da takwarorin karkashin tsarin La Masia na kulaf din. Kana kulaf din na Barcelona ne zai dauki dukkanin nauyin 'yan wasan.
Kaza lika Barcelona na shirin kafa makarantar horas da 'yan wasan kwallon kafa irin ta ta farko a nan kasar Sin nan gaba cikin wannan shekara, a dai kan tsarin horaswa na La Masia. Wannan tsari dai ya samar da taurarin 'yan wasa da dama wadanda suka yi fice a duniyar kwallon kafa, kamar shahararren dan wasan kulaf din Lionel Messi.
Ana dai kallon wannan mataki da Barca ke dauka a matsayin daya daga manufar shugabannin kasar Sin ne, a fannin sauya tsarin kwallon kafa da shugabannin kasar suka alkawarta aiwatarwa.
Tsare-tsaren sun kunshi irin matakan da ake fatan dauka na bunkasa kwallon kafa a Sin, ciki hadda samar wa kasar damar shiga gasar cin kofin duniya, da ma sauran matakai na bunkasa ci gaban harkar kwallon kafar baki daya.
An ce kulaf din na Barca na cikin wadanda suka shige gaba a fannin hadin gwiwa da mahukuntan kasar Sin, wajen tabbatar da nasarar wannan buri. (Saminu Alhassan)