150702-yan-wasa-baki-sun-kawo-sabon-yanayi-ga-wasan-kwallon-kafa-a-nahiyar-asiya-Bello.m4a
|
Mun dai san cewa Bhutan karamar kasa ce, don haka ba abun mamaki ba ne ganin raunin kungiyar kwallon kafar ta. Amma a wannan karo ba dukkanin kungiyoyin kananan kasashen da ke nahiyar Asiya ke cikin irin wannan yanayi ba.
Ga misali, Guahan ta lashe Indiya da ci 2 da 1, yayin da Philippines ta lashe Yemen da ci 2 da nema.
A wannan karo, bayan da tsibirin Guahan ya ci wasanni 2 a jere, ya zama a matsayin farko a rukunin D, sa'an nan wadanda suke biye da shi a baya sun hada da Iran da Omen, wadanda ke da karfi bisa tarihin wasanni na nahiyar Asiya. Haka zalika, a rukuni na E ma, wasu kungiyoyi sun bada mamaki, ganin yadda Singapore ta kasance ta farko a rukunin, bayan ta yi kunnen doki da kungiyar Japan, wadda ta kasance kungiya mafi karfi a nahiyar Asiya.
Irin sauyin yanayin da aka samu a fannin wasan kwallon kafa a nahiyar Asiya bawai saboda wadannan kananan kasashe sun samu hakikanin ci gaba a fasahar taka leda ba ne, a'a ainihin dalilin shi ne wasu kasashe a Asiya, sun rungumu sabuwar manufar shigo da 'yan wasa 'yan kasashen waje, inda suke canza musu shaidar kasar haihuwa, su kuma rika buga musu wasanni. Irin wadannan 'yan wasa da dama sun fito ne daga kasashe masu kwarewa su ne ke canza salon kwallon kafa a kasashen da suka koma.
Ga misali, kungiyar tsibirin Guahan ta yi karo da rashin nasara a wasanni 27 da ta buga a jere tare da sauran kungiyoyin kasashen nahiyar Asiya. Amma bayan da dan kasar Birtaniya Gary White ya zama babban kocin kungiyar, ya shigar da manufar kungiyar ta shigo da 'yan wasa 'yan kasashen Amurka da Canada, musamman ma wadanda ke da asali a tsibirin na Guahan. Saboda haka, kungiyar Guahan ta yanzu, kusan dukkan 'yan wasanta sun zo ne daga nahiyar Amurka, matakin da ya yi matukar kara karfin kungiyar.
Kungiyar Philippines kuwa, ita ma hakan take. Domin a yanzu cikin 'yan wasa 23 dake taka leda a kungayar kasar, 'yan wasa 4 kacal ne haifaffun kasar ta Phillippines. Sauran 'yan wasan dukkansu sun kasance kwararrun 'yan kwallon ne daga kulaflikan kasashen Birtaniya, Jamus, Holland, Sin da dai sauransu.
Yayin da Guahan ta ke mai da hankali kan arewacin nahiyar Amurka, ita kuma Philippines take kokarin neman fitattun 'yan wasa daga kasashe daban daban, ita kuma Timor-Leste ta yi amfani da matsayinta na daya daga cikin yankuna masu amfani da yaren Portugal ne, wajen kokarin janyo hankalin 'yan wasan kasar Brazil, wadanda su ma suke magana da yaren Portuguese.
Kungiyoyin da muka ambaci sunayensu a sama, sun fara kokarin shigo da 'yan wasa baki ne a shekarun baya-bayan nan. Amma kungiyar Hong Kong ta kasar Sin ta dade tana bin wannan manufa. Yanzu haka idan mun duba sunayen 'yan wasan kungiyar, za mu ga Festus Baise, dan asalin Najeriya ne, akwai kuma Jonathan Sealy dan kasar Birtaniya, da Christian Kwesi Annan, da Godfred Karikari da suka zo daga kasar Ghana, da dai makamantansu.
Game da manufar shigo da 'yan wasa baki zuwa cikin wata kasa, hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, tana da wasu ka'idoji guda 5.
Wato da farko ana bukatar a haifi dan wasan da ake son shigo da shi a kasar da ake neman ya koma cikinta. Sa'an nan na biyu, daya daga cikin iyayensa ya zama haifaffen wurin ne. Banda haka kuma ana bukatar daya daga cikin kakaninsa ya zamo haifaffen wurin da ake son dan wasan ya koma ne.
Kaza lika ana son bayan dan wasan ya kai shekaru 18 da haihuwa, ya kasance ya taba zama a kasar ta biyu har tsawon shekaru 5 a jere. A karshe ana bukatar cewa dan wasan ya zamo bai taba taka leda ga wani kulaf cikin sauran tsare-tsaren wasannin kasa da kasa ba.
Sai dai wannan manufar da hukumar FIFA ta tsara amfani da ita na gamu da matsaloli, inda ake burin yiwa tsarin gyaran fuskarta. Ga misali, a shekarar 2009, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Aljeriya, ta yi kira da a soke kayyade shekarun dan wasan da ake son shigo da shi. Daga baya an yarda da kiran ta, aka kuma zartas da shi a matsayin wata sabuwar dokar hukumar FIFA.
Sa'an nan a bangaren nahiyar Asiya, kungiyoyin nahiyar sun fara shigo da 'yan wasa baki ne a farkon shekarun 1990. A shekarar 1993, kasar Japan ta sauya wani dan asalin kasar Brazil ya zama dan kasar Japan, ta yadda ya iya halartar wasan share fagen gasar cin kofin duniya a madadin Japan.
Sai dai cikin shekaru 10 da suka wuce, cikin kasashen nahiyar Asiya, wadda ta fi yawan amfani da 'yan wasa baki ita ce kasar Qatar. Kasar dake da dimbin albarkatun mai, ta ware makudan kudi don samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, saboda haka ba shakka tana iya janyo hankalin fitattun 'yan wasan kasashe daban daban bisa albashi mai tsoka.
An ce yanzu kasar ta kafa wata cibiyar horar da matasa 'yan Afirka, don su zama fitattun 'yan wasan kwallon kafa a nan gaba, wadanda kuma za su samar da gudunmawa ga fasahar wasan kwallon kafa ta kasar. Shirin na ta mai taken "Burin nahiyar Afirka a fannin wasan kwallon kafa" zai baiwa yara 50 daga kasashe 7 na nahiyar Afirka damar samun horo mai kyau, wadanda a nan gaba za a karbe su don su zama 'yan kasar Qatar. (Bello Wang)