A ranar Litinin ne hukumar ta CAF ta sanar da hakan, inda ta ce za a gudanar da walawalar ne a birnin Alkahira na kasar Masar, da misalin karfe 11 rana bisa agogon wurin.
A ajin maza, kasashen da za su kara da juna sun hada da mai masaukin baki wato kasar Congo, da Burkina Faso, da Masar, da Ghana. Sauran su ne Najeriya, da Senegal, da Sudan da kuma Zimbabwe.
A bangaren mata kuwa, akwai kasashen Congo, da Kamaru, da Cote d'Ivoire. Sai kuma Masar, da Ghana, da Najeriya, da Afirka ta Kudu da kuma Tanzaniya.
Za a gudanar da wasannin gasar "All-Africa Games" ne tsakanin ranekun 4 zuwa 19 ga watan Satumbar dake tafe.(Saminu Alhassan)