Cikin manyan baki da suka halarci wannan kwallo hadda shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama, kana manyan 'yan wasan Afirka kamar su Samuel Eto'o na Kamaru, da George Boateng, da Emmanuel Adebayor na Togo, da kuma Guiseppe Coluci sun buga wannan wasa mai matukar tarihi.
Appiah dai ya kammala tamaula bayan shafe shekaru kusan 20 tauraruwar sa na haskawa. 'Yan kallo na yi masa lakabi da 'Tornado', ya kuma jagoranci tawagar kasar Ghana zuwa gasar cin kofin duniya na farko da kasar ta halarta a matsayin kyaftin din ta a shekarar 2006, gasar da ta gudana a kasar Jamus. Sai kuma a shekarar 2010, lokacin da kulaf din kasar Black Stars ya kai ga wasan kusa da kusan na karshe a gasar cin kofin duniya da ta gudana a Afirka ta Kudu.
Appiah ya zamo misali ga masu burin taka leda a kasar sa, duba da yadda ya fara tun daga yarinta, zuwa lokacin da ya kai ga bugawa kulaf din Juventus na kasar Italiya wasa.
Dan wasan wanda ya bugawa Black Stars wasa har karo 67, ya ce yayi farin ciki game da irin karramawar da 'yan kasar sa suka nuna masa a lokutan wasa da ma a wajen fili. Cikin wasannin da ya takawa kasar sa, Appiah ya jefa kwallaye 14 a raga, tare da karfafa gwiwar kungiyar ta Black Stars, da ma daukacin matasan 'yan kallon kasar ta Ghana.(Saminu Alhassan)