Robinho mai shekaru 31 da haihuwa ya zamo dan wasa mai cin gashin kan sa, bayan da ya kammala kwangilar ta sa, kafin hakan ya shafe shekarar bara yana taka leda a kulaf din Santos a matsayin aro, inda a yanzu kulaf din na Santos shi ma ke cikin masu zawarcin dan wasan.
Da yake tsokaci game da wannnan batu, yayin wata tattaunawar da wakilin gidan Radion Globo a ranar Litinin, babban manajan kulaf din Cruzeiro Barbosa, ya ce kocin Guangzhou Evergrande Luiz Scolari, ya share fage ga 'yan wasan dake zuwa kasar Sin taka leda daga kasar Brazil.
Barbosa ya ce ko shakka babu idan har Scolari da kungiyar sa ta Guangzhou Evergrande suna da bukatar daukar Robinho, to kuwa kulaf din sa ba shi da damar yin takara, duba da irin kudin da Guangzhou Evergrande din za ta yi wa dan wasan tayi.
A ranar Lahadin nan ne dai Robinho ya koma gida, bayan da Paraguay ta doke Brazil a wasan kusa da kusan na karshe, na cin kofin Copa America, a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Rahotannin na cewa Robinho wanda tsohon dan wasan Real Madrid da Manchester City ne, na da kulaflika da dama dake zawarcin sa, ciki hadda wasu dake kasar Amurka.(Saminu Alhassan)