in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Amurka ta wayar tarho
2015-07-21 11:25:20 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama ta wayar tarho bisa gayyatar hakan daga fadar White House.

Yayin zantawar tasu, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa a halin yanzu, ana samun bunkasar hulda tsakanin kasashen Sin da Amurka yadda ya kamata, kana kasashen biyu na musayar ra'ayi, da kokarin cimma daidaito game da manyan batutuwan kasa da kasa, da na yankuna, da kuma na duniya baki daya.

A watan Satumbar bana ne dai ake sa ran shugaba Xi zai kai ziyara Amurka bisa gayyatar da shugaba Barack Obama ya yi masa.

Game da hakan Mr. Xi ya yi fatan amfani da wannan dama wajen ingiza fahimtar juna, da sada zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu, domin kara bunkasa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasashen Sin da Amurka sun yin musayar ra'ayi, da cimma daidaito matuka a fannin gudanar da shawarwarin nukiliyar Iran, matakin da ya nuna sabuwar huldar da kasashen biyu suka kafa. Kana kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Amurka, da sauran bangarorin masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da gudanar da yarjejeniyar, da kuma kudurin da kwamitin sulhun MDD ya yanke.

A nasa bangare, shugaba Obama ya ce shi da jama'ar kasar Amurka na dakon ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gudanar a watan Satumba. Yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da kokarin shirya wannan ziyara.

Kaza lika, Obama ya bayyana cewa kasar Sin na taka muhimmiyar rawa, wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni. Har wa yau Amurka ta godewa kasar Sin bisa babbar gundummawar da ta bayar game da wannan batu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China