in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Indonesiya game da hadarin jirgi
2015-07-02 19:15:38 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Indonesiya Joko Widodo, game da hadarin jirgin saman yakin kasar wanda ya sabbaba rasuwar mutane da dama.

Shugaban Xi ya aike da sakon ne a ranar Alhamis din nan, inda ya bayyana jimamin faduwar jirgin a wani wuri dake kusa da birnin Medan na tsibirin Sumatera a ranar 30 ga watan da ya gabata.

A madadin gwamnatin Sin da jama'arta, shugaba Xi ya jajantawa daukacin al'ummar kasar ta Indonesiya bisa aukuwar wannan hadari, tare da gabatar da ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China