in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sassa daban daban na kasar Rasha sun jinjinawa bayanin shugaba Xi
2015-05-08 09:27:53 cri

Kafin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Rasha don halartar bikin tunawa da ranar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kiyaye kasar Rasha, an wallafa wani bayani mai taken "tunawa da tarihi da kafa makoma" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta a Jaridar "Russian Gazeta" ta kasar Rasha, inda ya waiwayi tarihin hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha, kuma ya nuna niyyar bangarorin biyu ta kiyaye sakamakon yakin duniya na biyu, da yin hangen nesa kan kyakkyawar makomar bil Adam. Bayan da aka gabatar da bayanin, jami'an gwamnati da masana da kuma fararen hula na kasar Rasha sun mai da hankali sosai kan bayanin,inda manyan kafofin watsa labaru na kasar suka rika ruwaito wannan bayani.

Jama'a daga sassa daban daban na kasar Rasha sun bayyana cewa, shugaba Xi bako ne mafi muhimmanci cikin mahalarta bikin, saboda yadda ya ke ba da muhimanci ga batun da ya shafi tarihi da makoma. A cikin sabon halin yanzu, kasashen Sin da Rasha sun hada kai wajen tunawa da nasarar da aka samu a yakin duniya na biyu wadda ke da ma'ana sosai.

Mataimakin shugaban hukumar gabashin Asiya ta cibiyar kimiyya ta kasar Rasha Andrei Ostrovsky ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubaloli da dama a duniya, lamarin da ya sa ake bukatar kasashen Rasha da Sin da su yi hadin gwiwa sosai a karkashin tsarin kwamitin sulhu na MDD domin tinkarar wasu batutuwa, kamar kungiyar IS, da 'yan ta'adda, da kuma halin kiki-kaka da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka. A cewar masanin, kasar Sin na kara taka rawar gani a kokarin kula da batutuwan da suka shafi kasa da kasa, hakan zai inganta hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha a duniya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China