in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya murnar bude taron shugabannin kungiyar AU a karo na 25
2015-06-15 08:56:50 cri

A jiya Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa kasashen Afrika da kuma jama'arsu sakon taya murnar bude taron kolin shugabannin kungiyar tarayyar kasashen Afrika (AU) a karo na 25.

A cikin sakonsa, Xi Jinping ya nuna babban yabo ga babbar gundummawar da kungiyar AU ta bayar wajen raya kasashen Afrika da bunkasa sassa daban daban na Afrika da kuma harkokin kasa da kasa da na yankuna daban daban, kana ya jinjinawa shirin raya nahiyar nan da shekarar 2063 da kungiyar AU ta gabatar, yana fatan kasashen Afrika da kuma jama'arsu za su kara samun sakamako mai kyau wajen inganta rayuwar al'umma da neman samun bunkasuwa cikin lumana.

Ban da haka kuma, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ba ma kawai hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika za ta kawo moriyar bunkasuwarsu da kansu ba, har ma za ta inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa.

Kasar Sin za ta ci gaba da tsara sabbin manufofin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afrika domin neman samun bunkasuwa tare bisa ka'idojin nuna sahihanci da gaskiya, ta yadda za a ciyar da huldar bangarorin biyu gaba da kawo moriya ga jama'arsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China