Da farko, a madadin gwamnatin Sin, shugaba Xi ya mika sakon murnar kaddamar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar. Sannan ya yi nuni da cewa, Sin ta yi tayin kafa bankin AIIB ne, da nufinn ci gaba da inganta habakar muhimman ababen more rayuwa a kasashen Asiya da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, don cimma burin samun bunkasuwa tare. Wannan yarjejeniya ta samu karbuwa daga kasashen Asiya da sauran kasashen duniya.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, yau, mambobin kasashen sun bi turbar akidar hadin gwiwa da bude kofa ga sauran kasashe don daddale yarjejeniyar.
Ya ce, muddin aka ci gaba da bin akidar hadin gwiwar bangarori daban daban,babu makawa za a kafa wani sabon dandalin samun moriyar juna, don kara ba da gudummawa ga kokarin da ake na samar da muhimman ababen more rayuwa a kasashen Asiya.(Bako)