in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sham: Kungiyar IS ta kashe fararen hula fiye da dari a tsohon birnin Palmyra
2015-05-25 15:29:25 cri

Gwamnatin kasar Sham ta ce kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta hallaka jama'a da dama a tsohon birnin Palmyra dake tsakiyar kasar, a hare-haren da suka haifar da kisan fararen hula fiye da dari daya.

Kamfanonin dillancin labaru na kasar Sham sun cewa kungiyar ta kashe a kalla fararen hula 400 a birnin Palmyra, ciki har da mata da yara, bisa dalilin goyon bayan su ga shugaba Bashar Assad, da kin karbar umurni daga kungiyar ta IS.

Kaza lika gwamnatin ta fayyace cewa, cikin wadanda suka rasa rayukan su akwai ma'aikatan hukumomi, da na kamfanonin gwamnatin, kana akwai mutane fiye da dubu daya, wadanda kungiyar ta hana fito daga birnin na Palmyra.

Tuni dai firaministan kasar Sham Wael al-Halki ya yi Allah wadai da matakin da kungiyar ta IS ta dauka, yana mai zargin wasu kasashe masu karfi da ci gaba da marawa kungiyar baya a fannin hada-hadar kudi, da aikin soja a asirce. Daga nan sai ya yi kira ga kasashe daban daban da su dakatar da kowane irin goyon baya da suke baiwa kungiyar ba tare da wani bata lokaci ba.

A wani ci gaban kuma, sojojin kasar Iraki sun tabbatar da fadawar birnin Al-Walid dake matsayin muhimmiyar tashar kan iyakar kasar ta Sham hannun dakarun kungiyar ta IS, kuma tuni sojojin Iraki suka janye daga birnin. Baya ga wannan birni, tuni kungiyar ta kuma kwace wata tasha ta daban mai suna Al-Tanf dake kasar ta Sham.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China