in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta fara horas da dakaru 'yan adawan kasar Sham
2015-05-08 15:53:53 cri

Ministan tsaron kasar Amurka Ashton Carter, ya bayyana cewa sojojin Amurka, sun fara ba da horo ga dakarun 'yan adawa na kasar Sham, domin tunkarar mayakan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.

Ashton Carter ya bayyanawa wani taron manema labaru da aka gudanar cewa, bangaren sojan kasar Amurka ya fara ba da horo ga dakaru 'yan adawa kimanin 90 a fannin dabarun yaki, kana an samar musu da kananan makamai.

Kaza lika horon ya kunshi taimakawa dakarun kasar Sham wajen yaki da 'yan kungiyar IS dake tada kayar baya, da ayyukan ta'addanci a kasar ta Sham.

Bugu da kari Carter ya ce idan an yi dauki ba dadi tsakanin dakaru 'yan adawan da sojojin gwamnatin kasar Sham, Amurka za ta dauki nauyin kare wadannan mayakan 'yan adawa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China