in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Sham na ci gaba da dakile kungiyar Al-Nusra dake kudancin kasar
2015-04-22 11:19:09 cri

Kamfanin dillancin labaru na kasar Sham ya ba da labari a jiya Talata cewa, sojojin gwamnatin kasar Sham na ci gaba da kai hare-hare ga kungiyar tsattsauran ra'ayi ta Al-Nusra a jihar Deraa dake kudancin kasar Sham a wannan rana, inda suka dakile dakaru da dama.

Labarin ya ce, sojojin gwamnatin Sham sun hallaka makamai da motoci da kuma wuraren boya a yayin da suka dauki matakin soja a wasu sansanonin kungiyar Al-Nusra dake arewa maso gabashin jihar Deraa.

Kafin haka, kamfanin dillancin labaru na Sham ya ba da labari a ranar 20 Litinin cewa, sojojin gwamnatin Sham sun samu babban ci gaba a arewa maso gabashin jihar Deraa, inda suka mamaye wasu kananan garuruwa, da yanke muhimmiyar hanyar jigilar dakaru da makaman da 'yan kungiyar adawa suka fasa kwauri daga birnin Jordan zuwa jihar Deraa da yankin Ghouta dake gabashin birnin Damascus, babban birnin kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China