in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kare hakkin dan Adam ya damu game da ci gaba da rasa rayuka a rikicin kasar Sham
2015-06-24 10:55:34 cri

A jiya Talata ne aka gudanar da wani zaman tattaunawa, a gun taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD a karo na 29 a birnin Geneva, game da yanayin da ake ciki don gane da hakkin dan Adam a kasar Sham.

Yayin taron, shugaban kwamitin bincike kan batun Sham mai zaman kansa na MDD Paulo Sergio Pinheiro, ya bayyana cewa ana ci gaba da hallaka fararen hula a yayin hare-hare da ke aukuwa, don haka ya kamata gwamnatin kasar ta Sham, da kuma tsagin 'yan adawar kasar su dauki alhakin abin da ke faruwa.

Kaza lika Mr. Pinheiro ya yi karin haske game da halin da ake ciki a fannin jin kai a kasar Sham. Ya ce an shiga shekaru 5 tun fara gwabza fada a kasar ta Sham, kuma fararen hula masu dimbin yawa sun mutu, wasu kuma sun rasa gidajensu, a sakamakon kisan fararen hula da kuma mamaye su da bangarorin kasar biyu ke yi.

Mr. Pinheiro ya kara da cewa, matakan soja da gwamnatin kasar Sham ta dauka, sun yi matukar haifar da illa ga fararen hula, a daya bangaren kuma, dakarun 'yan adawa su ma na ci gaba da hallaka fararen hula, kana ba a samu sakamako ko kadan ba, game da aikin shiga tsakani ta hanyar diplomasiyya.

A yayin da ake tattaunawa game da wannan yanayi, wakilan kasashe kimanin 50 sun gabatar da jawabi, inda galibinsu ke ganin cewa yanayin jin kai a kasar Sham ya fi tsananta a cikin wannan karni na 21, inda mutane kimanin dubu 220 suka mutu, a yayin da kuma wasu miliyan 7.6 suka rasa gidajensu. Kana wasu mutanen miliyan 4 suka zama 'yan gundun hijira dake tserewa zuwa kasashen waje. A daya bangaren kuma mata da yara kanana ke cikin matsanancin hali na bukatar tallafin jin kai.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China