in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sham sun hallaka dakarun 'yan adawa da dama a arewacin kasar
2015-04-30 10:48:45 cri

Kafofin watsa labarun kasar Sham sun bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kaddamar da hare-hare da dama a jihar Idleb dake arewacin kasar, lamarin da ya haddasa kisan mayakan 'yan adawa da dama a yankin.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Sham SANA ya ba da labari cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kaddamar da farmakin ne a jiya Laraba, kan rukunin motocin kungiyar Al-Nusra a birnin Jisr Al-Shughour dake jihar Idleb, inda baya ga dakarun kungiyar da aka kashe, harin ya kuma yi sanadiyyar lalata motoci da dama.

Kazalika, wani gidan talabijin dake kasar ta Sham ya labarta cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kashe dakaru masu tsattsauran ra'ayi a wani wuri dake dab da wani asibitin dake kudancin birnin Jisr al-Shughour.

Kungiyar sa ido game da kare hakkokin bil Adam dake aiki a kasar Sham mai hedkwata a birnin London ta tabbatar da kaddamar da hare-haren, inda ta bayyana cewa sojojin gwamnatin kasar Sham sun kai farmaki ta sama, sau da dama kan sansanin kungiyar masu tsattsauran ra'ayi a jihar ta Idleb, inda suka kashe dakaru a kalla 10.

Kungiyar Al-Nusra dai reshe ce ta kungiyar Al Qaida dake da sansani a kasar ta Sham. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China