in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta kaddamar da wani sabon shirin yaki da Ebola
2015-06-18 10:37:06 cri
Cibiyar kasa ta yaki da cutar Ebola ta kasar Saliyo (NERC) ta sanar a ranar Talata da kaddamar da wani sabon shirin yaki da cutar Ebola a cikin wasu yankunan kasar biyu da suka fi fama da wannan annoba, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 10 a wasu kasashen yammacin Afrika.

A yayin wani taron manema labarai na ranar Talata, Palo Conteh, darektan cibiyar NERC, ya bayyana cewa aikin zai shafi guraben cutar na karshe inda cutar Ebola ke zamaninta a arewacin kasar Saliyo.

Wannan mataki na cikin tsarin marawa dokar hana fita da shugaban kasar Ernset Bai Koroma ya sanya hannu kanta a makon da ya gabata a yankunan Port Loko da Kambia. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China