in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola ta hallaka wani mutum a Saliyo
2015-05-22 09:56:09 cri

Cibiyar yaki da cutar Ebola a kasar Saliyo ta ba da labarai cewa, cutar Ebola ta hallaka wani mutum a asibitin Freetown, babban birnin kasar Saliyo.

Babban jami'in cibiyar Pallo Conte wanda ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai na mako-mako da cibiyar ta saba gudanarwa ya bayyana cewa, majinyacin mai suna Saidu Conteh, ya mutu ne mako guda bayan da iyalansa suka arce da shi daga asibitin.

Don haka ya gargadi jama'a cewa, duk wadanda suka guda daga wuraren da aka killace su sakamakon cutar ta Ebola ko suke kula da irin wadannan mutane a asirce, hakika za su sheka barzahu.

Ya ce, labarin da aka samu na mutuwar wani mutum da kuma wani da ake zaton ya kamu da cutar Ebola a Moyamba, mai tazarar kilomita 200 daga babban birnin kasar, ya mayar da hannun agogo baya kan nasarar da kasar ta samu na rashin samun wanda ya kamu da cutar cikin kwanaki 8. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China