Kakain ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Algeriya Abdelaziz Benali Cherif kamar yadda kamfanin dillancin labarai na APS ta ruwaito, yace wadannan munanan hare hare da 'yan ta'addan suka aiwatar a jajibirin wata mai tsarki na Ramadan ya bayyana irin mummunar aniyarsu.
An labarta cewa mayakan na Boko Haram sun kai hari ne a kauyuka biyu a kudancin Niger a daren Laraba, tare da hallaka mutane fiye da 30 galibin su mata da yara.