in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taka muhimmiyar rawa a yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar Iran
2015-07-15 13:42:51 cri

A jiya Talata 14 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif da babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro Frederica Mogherini suka bayar da hadaddiyar sanarwa cewa, kasar Iran da kasashen nan shida da batun nukiliyar Iran ya shafa wato Amurka, Ingila, Faransa, Rasha, Sin da Jamus sun cimma yarjejeniya game da batun nukiliya na kasar Iran a dukkan fannoni bayan da suka yi shawarwari na zagayen karshe har na tsawon fiye da rabin wata.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana wa 'yan jarida na Sin da na kasashen waje cewa, wannan rana ce mai muhimmanci a tarihi, inda aka kawo karshen shawarwarin da aka shafe kusan sheakaru 13 ana tafkawa game da batun nukiliyar kasar ta Iran, kuma kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan wannan batu.

Wang Yi ya yi nuni da cewa, abu mai muhimmanci da aka cimma a wannan yarjejeniya game da batun nukiliya na kasar Iran shi ne an kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya. Ya ce,

"Iran ta yi alkawari a siyasance cewa, ba za ta kera makaman nukiliya ba, kuma an yi amfani da yarjejeniyar kasa da kasa don ganin ta cika alkawarinta. Babu shakka, yarjejeniyar ta baiwa Iran ikon yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, matakin da ya bude wani sabon babi kan dangantakar dake tsakanin Iran da sauran bangarori daban daban."

Wang Yi ya bayyana cewa, ma'anar cimma yarjejeniyar ita ce, samun moriyar juna. Batun nukiliyar kasar Iran ya shafi muhimman muradun bangarori daban daban, muddin babu bangaren da ya amfana, hakika ba za a cimma wannan yarjejeniya ba, kuma yarjejeniyar ba za ta dore ba.

Bugu da kari Wang Yi ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar ta zama misali ga kasashen duniya kan warware manyan matsaloli ta hanyar yin shawarwari, wadda za ta bada misali yayin da ake yin kokarin warware sauran manyan matsalolin duniya ciki har da batun nukiliya na zirin Koriya, wannan kuma shi ne muhimmancin wannan yarjejeniya a wani bangare na daban da ya zarce batun nukiliyar Iran..

Wang Yi ya kara da cewa, babban kalubalen da za a fuskanta shi ne ko za a aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata ko a'a, ya ce,

"Hakika, cimma yarjejeniyar shi ne matakin farko na warware batun nukiliya na Iran, kuma za a aiwatar da yarjejeniyar ce cikin tsawon shekaru 10. A yayin da ake aiwatar da ita, kamata ya yi bangarori daban daban su kara yin imani da juna, wannan ne ginshikin aiwatar da yarjejeniyar. Kana bangarorin daban daban su kara fahimtar juna, da cika alkawarinsu, sannan su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, ta yadda za ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, da sa kaimi ga tabbatar da tsaro a yankin, da kuma kyautata dangantakar dake tsakanin bangarori daban daban."

Hakazalika kuma, Wang Yi ya ce, a matsayinta na wakiliyar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin ta san nauyin da ke kanta na kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, don haka ta yi kokarin shiga shawarwarin nukiliyar Iran. Kasar Sin ta yi la'akari da moriyar bangarori daban daban, da neman hanyar warware matsalar, kuma ta gabatar da ra'ayin Sin kan batun.

A mataki na gaba, akwai ayyuka da dama da ake bukata kafin a aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, kasar Sin za ta ci gaba da daukar alhakinta tare da bada gudummawa kan wannan batu.

Yanzu kasar Sin tana aiwarar da manufar "ziri daya da hanya daya", kuma kasar Iran tana daya daga cikin manyan kasashen dake hanyar siliki ta ratsa. Game da ko za a bude kofar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Iran bayan da aka cimma wannan yarjejeniya, Wang Yi ya bayyana cewa, idan har kasar Iran ta aiwatar da wannan yarjejeniya, za a yi kokarin soke wasu takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakabawa kasar Iran, wannan zai taimaka wajen raya dangantakar dake tsakanin kasar Iran da sauran kasashen duniya, ciki har da dangantakar dake tsakanin Sin da Iran. Wang Yi ya bayyana cewa,

"Muna fatan za a bude sabuwar makoma ta hadin gwiwar Sin da Iran ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma, ta yadda za a amfana wa jama'ar kasashen biyu, musamman jama'ar kasar Iran. A ganina, za a samu babban canji bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China