Madam Hua ta nuna cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayinta na neman sulhu a tsakanin bangarori daban daban. A shekarar ta 2006 ne aka shigar da kasar Sin cikin tsarin kasashe 6, sannan ta tura wakilanta zuwa shawarwarin da aka yi tsakanin wadannan kasashe 6 har sau 4, da wani taron kwararru kan batun. Haka kuma, a cikin wadannan shekaru da yawa da suka gabata, bangaren Sin ya yi kokarin yin mu'amala tsakaninsa da sauran bangarori daban daban, kuma ya yi kokarin neman sauran bangarori da su dauki matakai bisa hakikanin halin da ake ciki, ta yadda za a iya kulawa da abubuwa daban daban na bangarori daban daban domin lalubo shirin da ya dace, har ma kasar Sin ta fitar da shawara mai amfani domin kokarin kawar da sabane-sabanen da ke kasancewa a tsakanin bangarori daban daban da neman matsaya daya. Sakamakon haka, bangarori daban daban suka yaba wa kyakkyawar rawar da kasar Sin ke takawa kan batu. (Sanusi Chen)