in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da ake bukata a yayin da ake tattara kudi a cinikin Afirka ya kai dala biliyan 120
2015-07-14 14:08:29 cri
A jiya ne babban direktan hukumar ciniki ta duniya wato WTO Roberto Azevedo ya bayyana a birnin Addis Ababa dake kasar Habasha cewa, a yanzu haka babu tabbas a yanayin harkokin cinikayya a kasashe masu tasowa na Afirka, kuma gibin kudin ya karu daga dala biliyan 110 zuwa dala biliyan 120.

Roberto Azevedo ya bayyana haka ne a gun taron manema labaru a yayin taron kasa da kasa karo na uku na MDD game da tattara kudi da samun bunkasuwa, inda ya ce, fiye da kashi 80 cikin dari na harkokin ciniki a duniya na samun taimakon kudi ko lamuni iri daban-daban, amma har yanzu kasashe masu tasowa da ke yankin Asiya da Afirka na fama da mummunan tasirin da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya haifar a shekarar 2008, sannan kudaden da ake samarwa harkokin cinikayya ba su koma daidai ba.

Hakazalika kuma, Azevedo ya ce, a kokarin da ake na taimakawa kasashe maso tasowa na Afirka wajen samar da kudade ga harkokin cinikayya, hukumar WTO ta kara yin hadin gwiwa tare da hukumomin hada-hadar kudi na yankin a shekarun baya baya nan, da fadada kafofin saukaka harkokin cinikayya tsakanin kasashe masu tasowa, da dora muhimmanci ga yin ciniki tare da kananan kamfanoni da masu zaman kansu na Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China