'Yan kasar Sin da suka fito daga kananan kabilu na kasar Sin da aka tura sun kasance 'yan ci rani da suka yi tafiya ba su da takardu da zama a kasar Thailand ta hanyar wasu hanyoyi daban daban, in ji kakakin a yayin wani taron menama labarai.
Madam Hua Chunying, ta yi wadannan kalamai a yayin da take amsa tambayar da ta shafi tuso keyar 'yan kasar Ouigour a ranar Laraba daga kasar Thailand, lamarin da ya janyo yin alla wadai a wasu kasashen duniya, kamar kasashen Amurka, Turkiya da kuma nuna damuwar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD.
A cewar kakakin, wasu gwamnatoci da wasu kungiyoyin kasashen waje, tare da rashin fahimtar abubuwan da ke faruwa, sun dauka cikin rashin sani wadannan 'yanci rani da ba takardu a matsayin wasu 'yan gudun hijira, tare sukar lamarin huldar dangantaka da ke tsakanin Sin da Thailand bisa aiwatar da doka, ta hanyar sanya siyasa kan batun.
Wadanda ke amfani da gudun hijira ba bisa doka ba, sumogal, take dokokin kasa da kasa, za su iya kawo illa ga kokarin hadin gwiwa baki daya a cikin yaki da gudun hijira ba bisa doka ba. Ba za mu yarda da wannan ba har abada, in ji madam Hua.
Haka kuma ta yi alla wadai, da tashe tashen baya bayan nan kan al'umma da kungiyoyin kasar Sin da Thailand, a kasar Turkiya dalilin tuso keyar 'yan kabilar Ouigour daga kasar Thailand. (Maman Ada)