Hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD ce ta tabbatar da hakan a ranar Juma'a 21 ga watan nan. Hukumar ta UNHCR ta ce yanzu haka jimillar adadin wadanda suka tsallaka zuwa Kamarun ta kai mutane 35,142.
Tun dai cikin watan Disambar shekarar 2012 ne, kungiyar Seleka ta mabiya addinin Musulunci ta fara kaddamar da hare-hare a kasar, matakin da ya sanya rikicin rikidewa zuwa na kabilanci, bayan da a baya bayan nan, 'ya 'yan kungiyar Anti-Balaka ta Kiristoci suka dauki makamai.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, dubban mutane ne suka rasa rayukan su tun fara rikicin, wanda kuma ya jefa dubban al'ummar kasar cikin mawuyacin hali. Baya ga al'ummun kasar kusan miliyan guda da suka rasa matsuguni, akwai kuma mutane kimanin miliyan Biyu da rabi, da ke bukatar agajin gaggawa.
Tuni dai babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, da sauran manyan jami'an majalissar suka ayyana bukatar da ake da ita, ta kara yawan tallafin da al'ummar wannan kasa ke samu daga kasashen duniya. Ciki hadda batun zakulo hanyar dakatar da kisan fararen hula, da ragewa al'ummar da rikicin ya daidaita radadin halin da suke ciki. (Saminu Alhassan Usman)