in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane dubu 15 a kaiwa kawanya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
2014-02-26 10:58:50 cri
Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya bayyana a ranar 25 ga wata cewa, mutane kimanin dubu 15 ne aka yiwa kawanya a wasu sassa 18 da ke kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, matakin da ka iya jefa rayuwar su cikin hadari.

Wannan dai mataki ya sanya hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta yi kira da dakatar da kaiwa fararen hula hare-hare.

Har wa yau hukumar ta UNHCR ta labarta cewa, akasarin mutanen su dubu 15 musulmai ne dake arewa maso yammaci, da arewa maso gabashin kasar, ciki hadda sassan da ke hedkwatar kasar Bangui.

Nesirky ya ce, ko da yake hukumar UNHCR da sauran hukumomin jin kai na daukar matakan ba da kariya, duk da haka ba su kai ga daidaita wannan matsala ba. Har wa yau, hukumar ta yi kira ga dukkanin dakaru masu dauke da makamai da su dakatar da hare-hare kan fararen hula, tana mai kira da a kara yawan sojojin kasa da kasa zuwa kasar.

A sanarwar da hukumar tsara shirin abinci ta MDD ta fitar kuma, ta ce, yanzu haka dubban fararen hula, na tserewa daga kasar ta Afirka ta Tsakiya zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita, kuma suna matukar bukatar taimako, matakin da ka iya haifar da matsala a shiyyar baki daya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China