Rahotanni sun bayyana cewa zaunannen kwamitin majalissar ne ya zartas da kudurin amincewa da hakan, yayin taron da yake gudanarwa a watanni biyu biyu.
An dai cimma yarjejeniyar samarwa bankin na NDB kudade ne a ranar 15 ga watan Yulin shekarar bara, a yayin taron kolin kungiyar ta BRICS, batun da ya samu amincewar daukacin kasashe 5 mambobin kungiyar, wato kasashen Brazil, da Russia, da India, da Sin da kuma Afirka ta Kudu.
A cewar ministan kudin kasar Sin Lou Jiwei, bankin zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin BRICKS ta fannin hada-hadar kudi, tare da fadada samar da ababen more rayuwa, da wanzar da ci gaba tsakankanin kasashe masu tasowa.