Wani jami'in ma'aikatar harkokin waje ta Sin ya bayyana cewa, a cikin yayin taron kolin, za a yi shawarwari kan muhimman batutuwa biyar. Wato, na farko, yin shawarwari kan kara kyautata ayyukan kungiyar SCO, da kiyaye zaman lafiya a shiyya-shiyya, da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakaninsu a fannin tattalin arziki. Na biyu, yin musayar ra'ayi kan manyan harkokin duniya da na shiyya-shiyya. Na uku, kyautata hadin gwiwa tsakanin kasashe masu sa ido na kungiyar SCO da kasashe masu yin shawarwari da su. Na hudu, tabbatar da kasar da za ta ba da jagoranci a kungiyar SCO daga shekarar 2014 zuwa ta 2015. Na biyar, sa hannu da kuma gabatar bayar da sanarwar Dushanbe.(Fatima)