in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta ba da shawara ga kasashen duniya da su yi amfani da maganin Sin wajen tantance cutar Ebola
2015-05-15 10:47:07 cri
Kwanan baya, wani kamfanin kimiyya da fasaha na birnin Shanghai na Sin ya kirkiro da wani sabon magani don tantance cutar Ebola, kuma hukumar WHO ta amince da amfanin maganin, inda ta sanya shi cikin jerin sunayen magungunan da za ta saya, sannan ta shawarci duk kasashen duniya da su yi amfani da shi don tantance cutar Ebola.

Don yaki da cutar Ebola da ta barke a Afrika, hukumar WHO ta yi tayin samun maganin tantance cutar Ebola. Yanzu, ta amince da magunguna 4, bisa alkaluman da aka samu, an ce, a cikin duk wadannan magunguna 4, wannan maganin da kamfanin Shanghai ya kirkiro yana da amfani kwarai, kuma zai iya tantance wanda ya kamu da cutar Ebola cikin sauri.

Bisa labarin da aka samu, wannan magani ya samu takardar amincewa ta CE daga kungiyar EU, abin da ya sa ya zama magani na farko da ya samu wannan izni wajen tantance cutar Ebola. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China