Mr. Wang ya bayyana hakan ne yayin wani kwarya-kwaryar taron da aka shirya a M.D.D. karo na 68, musamman ma domin dakile cutar Ebola, inda ya ce ya kamata kasashen duniya su karkata hankulansu zuwa ga yaki da cutar, da kuma sake gina yankunan da ta yiwa ta'adi.
Wang Min ya ce, Sin na kokarin tattaunawa da kasashen da abun ya shafa, a wani mataki na tsara shirye-shiryen da suka dace a fannin hadin gwiwa tsakaninsu. Haka kuma Sin ta yi shawarwari da kungiyar AU, don kafa cibiyar yaki da cutar a nahiyar Afirka, tare da gudanar da tarurrukan horaswa 12 a nahiyar, a wannan shekara ta bana.
Wang Min ya kara da cewa, Sin ta ba da kudin karo-karo da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 6, ga asunsun da MDD ta kafa, don taimaki kasashen Afrika wajen yaki da cutar, kuma tana shirin ba da karin kudade a nan gaba. (Bako)