in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Canada da Amurka za su fidda maganin yaki da Ebola
2015-06-11 10:05:31 cri

Gwamnatin kasar Canada a ranar Laraban nan ta ce, ta saka hannu a kan wata kwangila ta kimanin kudin dala miliyan 4.5 da wani kamfanin samar da magunguna na Amurka Mapp Biopharmaceutical domin sarrafa maganin Zmapp Monoclonal antibody wato MAB, maganin kariya daga cutar Ebola da ta yi mummunar barna a yammacin Afrika.

Ministan kiwon lafiya na Canada Rona Ambrose a cikin wata sanarwa ya yi bayanin cewa, kasarsa ta samar da wadatattun kudaden ba da taimako a bangaren kiwon lafiya, jin kai da tsaro a kan Ebola a gida da kuma wajen, saka jari a cikin wannan fasaha mai alamun nasara ya karfafa karfinsu na iya tunkara cikin gaggawa na ba da kariya ga 'yan kasar.

Zmapp dai, hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta riga ta amince da shi don gwaji a asibitocin kasar, da kuma kasashen yammacin Afrikan, kuma ya nuna tabbaci idan aka yi amfani da shi a kan wadanda suka kamu da cutar.

Maganin na Zmapp da kamfanin samar da magunguna na Mapp Biopharmaceutical suka kirkiro ya yi amfani da wassu sinadarai wato MAB guda 2 da masanan kimiyya suka gano a dakin gwajin magungunan hukumar binciken magunguna ta kasar Canada, da kuma wani guda 1 da aka gano a cibiyar binciken magunguna a kan cututtukan yaduwa ta sojin Amurka.

Wannan kwangila dai ta ba da dama ga Canada wajen samar da maganin Ebola, curtar da ta hallaka mutane kusan 11,158 daga cikin mutane 27,237 da suka kamu da ita, in ji wani sabon rahoton da hukumar kiwon lafiya ta MDD wato WHO ta fitar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China