Masoya tawagar dauke da furannin tarbar baki sun rika shewa, da nuna farin ciki ga babbar nasarar da 'yan wasan na kasar Sin suka samu.
An dai fidda kungiyar ta Sin ne a wasan su da takwarar ta ta Amurka, inda Amurkan ta jefawa Sin kwallo daya mai ban haushi. Wannan ne dai karo na biyu da kulaflikan kasashen Sin da Amurka suka buga wasa a gasar cin kofin duniya, inda suka fara haduwa a shekarar 1999.
Gabanin haduwar su a wannan karo, Sin ta buga wasa da ya yi matukar kayatarwa tsakanin ta da kasar Canada.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa masu tarbar 'yan wasa sun rika kiran sunayen 'yan wasan daya-bayan-daya, daidai lokacin da suke sakkowa daga jirgin sama, tare da kocin su Hao Wei, da sauran 'yan tawagar 'yan wasan. Kafin daga bisani a mikawa kowannnen su furannin karramawa. Kana 'yan kallon sun rika daukar hotuna tare da kyaftin din kungiyar Wu Haiyan.
Game da irin karbar da 'yan wasan suka samu, kocin su Hao ta bayyana matukar jin dadin ta, tama mai cewa masu sha'awar kwallon kafa Sinawa sun yi matukar karrama su.
Kaza lika Hao ta ce gasar da suka shiga ta wannan karo ta ba su damar kara kaifafa kwarewar su, tare da cimma manyan nasarori, don haka ta yi fatan gogewar da suka kara samu a wannan lokaci, za ta ba su damar daga matsayin kasar a fannin taka leda a nan gaba.
Da take tsokaci game da wannan lamari, Wang Wen wadda ita ce shugabar kungiyar masu goyon bayan kulaf din na kasar Sin, ta shaidawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ya kamata a dada baiwa harkar ci gaban kwallon kafar mata kulawar da ta dace.
Wang ta ce ko wane irin hali da ake ciki, na nasara ko akasin haka, ya zama wajibi a ci gaba da bunkasa kwallon kafar mata, kuma dole ne a kara martaba, tare da karfafawa 'yan wasan gwiwa.
Yanzu haka dai 'yan wasan tamaular na kasar Sin mata 'yan kimanin shekaru 23, za su samu kyautar zunzurutun kudi har yuan miliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka 160,000, kyautar da ta zamo mafi yawa da aka taba baiwa kungiyar a tarihi.(Saminu Alhassan)