Hakan ya baiwa Amurka nasarar shigewa gaba da ci 4 da 1 a zangon farkon na wasan, kafin kuma a kammala taka leda Amurka na da kwallo 5 Japan na da 2.
Lloyd dai ta zura kwallon farko ne cikin mintuna 3 na farkon wasan, sai kuma kwallon ta ta biyu, mintuna biyu bayan ta jefa ta farko a raga. Bayan kwallon Lauren Holiday ta 3 cikin minti na 14 ne kuma Lloyd ta kara ta 4, cikin minti na 16, kwallon da ta buga daga tsakiyar filin wasan.
Sai kuma kwallo ta 5 wadda 'yar wasar Amurka Heath ta kara a ragar Japan kafin a karkare wasan.
A bangaren Japan kuwa, Yiki Ogimi ce ta ramawa kungiyar ta kwallo daya cikin miti na 27. Sai kuma kwallon da 'yar wasan Amurka Julie Johnston ta ci garin su bisa kuskure cikin minti na 52.
Haka kuma aka tashi wasan na karshe Amurka na da kwallaye 5 Japan na da 2. Nasarar da ta baiwa Amukar damar daukar kofin na bana, wanda ya zamo na uku a tarihin kungiyar kwallon kafar mata ta kasar, kuma na farko bayan shekaru 16 ta na fafutikar daukar kofin. A shekarar 1999 ne dai Amurka ta dauki wannan kofi a karon karshe kafin wanda ta dauka a ranar ta Lahadi karshen mako.(Saminu Alhassan)