in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chile ta lashe Copa America ta bugun daga kai sai mai tsaron gida
2015-07-09 10:02:20 cri
A gasar Copa America kuwa, kasar Chile ce ta dauki kofin gasar na bana, kuma a karon farko a tarihin ta, bayan da 'yan wasan ta suka jefa kwallaye 4 a ragar Agentina, a bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda aka kammala Chile na da kwallo 4 Argentina na da kwallo 1.

An dai buga wasan karshen na cin kofin Copa America ne a ranar Asabar, inda Sanchez ya buga kwallon karshe ga Chile, bayan da kwallon Gonzalo Higuain na Argentina ta daki karfen raga, kana Golan Chile Claudio Bravo ya doke wadda Ever Banega ya buga.

Yanzu haka dai ta tabbata Chile ce zakarar gasar Copa America ta bana, ta kuma dauki wannan kofi ne a karon farko bayan halartar gasar a karo na biyar. Chile ta halarci wannan gasa ne a karon farko a shekarar 1987.

A bangaren kasar Argentina kuwa, a iya cewa kulaf din kasar ya rasa karin wata babbar dama ta daukar kofi a bana, bayan da Jamus ta doke ta a wasan karshe na cin kofin duniya da ya gudana a kasar Brazil a bara.

Yanzu haka dai shekaru 22 ke nan Argentina na hankoron samun damar daukar kofin kwallon kafar kasa da kasa. Wannan ne kuma karo na 27 Argentinar na halartar gasar ta Copa America, a baya kuma ta taba daukar kofin gasar har karo 15.

Yayin wasan na karshe dai shahararren dan kwallon Argentina, wanda kuma ke rike da lambar girmamawa ta Ballon d'Or har karo 4, wato Lionel Messi, bai samu damar gwada bajintar sa ba, duba da yadda 'yan bayan Chile suka katse masa damar samun kwallaye daga abokan wasan sa.

Manazarta na ganin rashin taka rawar gani ga kasar sa a manyan wasannin kasa da kasa, na iya zamewa Messi koma baya a tarihin kwallon kafar sa, idan aka kwatanta shi da sauran manyan 'yan kwallon duniya da suka yi fice a wannan fanni.

An dai kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin kasashen biyu, gabanin kammala karin lokaci da alkalin wasan Wilmar Roldan dan kasar Colombia ya yi, kafin kuma a kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China