in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barcelona ta dauki kofin zakarun Turai a karo na 4
2015-06-12 09:17:56 cri

Kulaf din Barcelona na kasar Sifaniya, ya lashe kofin kwallon kafa na zakarun turai, bayan da ya doke Juventus da ci 3 da 1.

'Yan wasan Barcelona Ivan Rakitic, da Luis Suarez, da kuma Neymar ne suka ciwa kulaf din na su kwallayen 3, a wasan karshe da aka buga a ranar Asabar din karshen mako a birnin Berlin.

Gabanin tafiya hutun rabin lokaci ne dai dan wasan Juventus Alvaro Morata ya farke kwallon farko da aka zurawa kulaf din sa. Sai dai hakan bai hana 'yan wasan Barcelona durawa Juventus din karin kwallaye 2 ba. Inda daga karshe dai Barcelona ta yi gaba da kofin na bana da gagarumar tazara.

Barcelona da Juventus dai sun kai ga wasan karshe ne a karo na 8 a tarihin su, yayin da kuma kowannen su ke fatan daukar kofin zakarun na Turai, wanda zai baiwa kowannen su damar kammala kakar wasannin bana da kofuna 3.

Da kuma wannan nasara kocin Luis Enrique, ya kammala lashe kofuna 3 a zangon farko na horas da Barcelona. Bisa tarihi Barcelona ne kulaf na farko da ya lashe kofuna 3 a kakar wasanni daya har sau biyu, wato a kakar shekarar 2009 da kuma kakar bana.

Bisa jimilla kulaf din ya lashe kulaflikan Turai 5, da na manyan kulaflikan Turai 1, da kuma na zakarun nahiyar Turai guda 4.

Barca ta tsawaita wa'adin kwantiragin Rodriguez

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta bayyana tsawaita wa'adin kwantiragin dan wasan gaban ta Pedro Rodriguez, wanda bisa sabon wa'adin taka ledar sa, zai kasance a kulaf din har ya zuwa watan Yunin shekarar 2019.

Kulaf din dai ya zartas da wannan kuduri ne kwanaki biyu, gabanin buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai. Wasu manazarta kwallon kafa sun bayyana mamakin daukar wannan mataki, ganin cewa Pedro na matsayi na 4, a bayan manyan 'yan gaban kungiyar, wato Leo Messi, da Luis Suarez and Neymar, ko da yake duk da shigewa gaba da wadannan taurari na kungiyar suka yi, Pedro ya samu nasarar ciwa kungiyar ta Barca kwallaye 11, ya kuma taimaka wajen cin wasu kwallayen 8.

Ana dai danganta daukar wannan mataki da Barca ta yi, da dalilai da suka hada da kasancewar kulaf din ba shi da damar dauko sabbin 'yan wasa a wannan lokaci na bazara, kana kasancewar shi kan sa Pedro bai nuna wata rashin gamsuwa da matsayin sa a kulaf din ba, duk kuwa da sha'awar da wasu kulaflikan Ingila kamar Arsenal, da Liverpool suka nuna na sayen sa.

Pedro wanda zai cika shekaru 28 a cikin wata mai kamawa, zai kammala sabuwar kwangilar sa da Barca yana da shekaru 32 ke nan. An kuma ce zai ci gaba da karbar Albashi kimanin dalar Amurka miliyan 165 a kowace shekara.

Baya ga Pedro, Barca ta kuma tsawaita wa'adin kwangilar ta dan bayan kulaf din Jordi Alba ya zuwa shekarar 2020.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China