in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai tafi Ufa na kasar Rasha domin halartar taro karo na 7 na shugabannin kasashen BRICS da taro karo na 15 na kwamitin kungiyar SCO
2015-07-06 20:08:44 cri
A yau ne a nan birnin Beijing, a yayin wani taron manema labaru da aka shirya, Mr. Cheng Guoping, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya shelanta cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai je Ufa na kasar Rasha domin halartar taro karo na 7 na shugabannin kasashen BRICS da taro karo na 15 na kwamitin shugabannin kasashen kungiyar hada kai ta Shanghai, SCO.

Game da taro karo na 7 na shugabannin kasashen BRICS, Mr. Cheng Guoping ya bayyana cewa, sau uku a jere da shugaba Xi Jinping ya halarci tarurrukan shugabannin kasashen BRICS, wannan ya alamta cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS. Babban jigon wannan taro na bana shi ne "dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen BRICS----abu mai muhimamnci ga bunkasuwar dukkan duniya".

Da ya juya game da taro karo na 15 na kwamitin shugabannin kasashen kungiyar SCO, Mr. Cheng Guoping ya nuna cewa, an dora wa wannan taron koli nauyin tsara yadda za a bunkasa kungiyar SCO da kuma muhimmin shirin neman bunkasuwa a fannoni daban daban tsakanin kasashe mambobinta. Don haka, wannan taro yana da muhimmanci kwarai ga kungiyar wajen neman ci gaba cikin hanzari, da taimakawa kasashe mambobin kungiyar wajen tinkarar kalubaloli da cimma burin karuwar tattalin arziki da dai makamatansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China