Shugaban na Sin ya jaddada hakan ne a wani taron jam'iyyar Kwaminis akan yaye talauci da cigaban tattalin arziki da zaman al'umma daga shekara ta 2016 zuwa 2020.
Yace mafi nauyin da kuma muhimmancin aikin da za'a cimma ganin al'umma sun wadata ta kowane bangare shi ne a kauyuka musamman ma wadanda suke fama da radadin talauci. Don haka a cewar shi ya kamata kwamitin jam'iyyar da jami'an gwamnati a dukkan matakai su zage damtse domin samar da wani shirin da zai rage radadin talauci.
Yace kasar Sin ta tsaida kudurin ganin daukacin al'umma sun wadata wanda daga cikin shirin ya kunshi wassu bukatu na musamman na ma'aunin GDP, da kudin shiga na kowane jari, adadin wadanda ake dauka da kuma yawan likitocin akan kowadanne mutane 1,000.
Taron dai an yi shi ne a wani kauye da ke fama da talauci a gundumar Guizhou a kudu maso yammacin kasar Sin.