in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Iraki sun kashe 'yan kungiyar IS 21
2015-01-18 17:08:30 cri
Bisa labarin da ma'aikatar tsaron kasar Iraki ta bayar, an ce, a ranar Asabar 17 ga wata, sojojin kasar sun samame a arewa da yammacin Iraki, inda suka harbe 'yan kungiyar IS 21, tare da kwace kauyuka 3. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki ta ba da labarin cewa, a wannan rana, an kai harin bom a birnin Baghdad, hedkwatar kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3, yayin da wasu mutane 18 suka jikkata.

Duk a wannan rana, ma'aikatar tsaron kasar ta ba da sanarwar cewa, a yayin gumurzu a arewa da kudancin birnin Tikriti, hedkwatar jihar Salahudin dake arewacin kasar, sojojin kasar sun harbe 'yan kungiyar IS 15, tare da lalata motocin dakarun da dama, amma sanarwar ba ta ce kome ba game da mutuwa da jikkatar sojojin Iraki.

Bayan haka, wani mutumin a jihar al-Anbar dake yammacin Iraki ya bayyana cewa, a wannan rana, sojojin sun yi musayar wuta tare da 'yan kungiyar IS a karkarar birnin Fallujah mai tazarar kilomita 60 daga birnin Baghdad, inda suka harbe dakaru 6, tare da raunata wasu 11. Bugu da kari, sojojin Iraki sun kwace kauyuka uku dake jihar al-Anbar.

Haka zalika, mMa'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki ta ba da labarin cewa, a wannan rana, wani babur mai dauke da bom ya fashe a wata kasuwa a yankin Sadr City dake gabashin birnin Baghdad, lamarin da ya haddasa mutuwar mazauna wurin uku, kana wasu mutane 18 suka ji rauni, a yayin da aka kai wasu mutane uku asibiti rai ga hannun Allah. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China