in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu muhimman sakamako a yayin shawarwari tsakanin shugabannin Sin da EU
2015-06-30 13:45:33 cri

A yammacin jiya ne shugabannin kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai wato EU suka yi shawarwari karo na 17 a babban zauren hukumar tarayyar Turai da ke Brussles, inda Li Keqiang, firaministan kasar Sin, Donald Franciszek Tusk, shugaban kungiyar tarayyar Turai, da Jean-Claude Juncker, shugaban hukumar kungiyar EU suka shugabanta.

An samu muhimman sakamako a yayin shawarwarin.

Bangarorin Sin da EU sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa dangane da shawarwarin da kuma batun daidaita sauyin yanayi, yayin da suka daddale wasu takardun fahimtar juna dangane da yin hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, kare ikon mallakar fasaha, manufofin shiyya-shiyya, harkokin kwastan da dai sauransu, sun kuma cimma daidaito a sassa da dama.

Har wa yau mista Li ya yi karin bayani kan ra'ayin kasar Sin game da yin hadin gwiwa a tsakanin Sin, EU da kasashen duniya ta fuskar karfin samar da kayayyaki, wanda bangaren EU ya yaba sosai.

Haka zalika, bangarorin 2 sun amince da ci gaba da bin manufofi da ka'idojin kundin tsarin MDD, tare da kara azama kan kyautata dokokin kasa da kasa cikin adalci.

Shugabannin sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan nukiyar Iran, yankin Gabas ta Tsakiya, Afghanistan da dai makamantansu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China